Chibok: Gwamnati ba ta gaza ba - Moro

Image caption Gangamin da mata suka yi a Abuja

Ministan harkokin cikin gidan Nigeria, Abba Moro ya bayyanna cewar babu adalci a dunga yin zargi kan cewar gwamnati ba ta yin kokari wajen ceto 'yan mata dalibai da aka sace a Chibok.

Fiye da makonni biyu kenan da aka sace 'yan mata dalibai su 230 a wata makaranta da ke garin Chibok a jihar Borno.

Mr Moro ya ce gwamnatin kasar ta kashe makudan kudade wajen kokarin ceto 'yan mata, amma saboda sarkakiyar lamarin ta fuskar tsaro, ba za su bada cikakkun bayanai ba game da yinkurin ceto 'yan matan.

Ya bayyana haka ne jim kadan bayan da daruruwan mata suka yi gangami a Abuja babban birnin kasar, inda suka bukaci gwamnati ta dauki matakan ceto 'yan matan.

Mr Moro kuma ya kara cewar an gano wasu karin 'yan matan Chibok din hudu a garin Monguno bayan da suka tsere daga hannun 'yan bindigar da suka sace su.

Masu sharhi na ganin cewar gwamnatin ta yi abin kunya na kasa ceto 'yan matan duk da cewar a yanzu haka akwai kusan 190 a hannun 'yan Boko Haram.

Karin bayani