An kara wa'adin taron kasa a Nigeria

Image caption Wakilai 400 ne daga sassa daban-daban na Nigeria ke mahawara

An kara wa wakilan babban taron kasa a Nigeria makonni shida domin su sami damar kammala shawarwarin da za su gabatar wa gwamnati.

Hakan na nufin za a kammala taron a ranar 31 ga watan Yuli na wannan shekarar a maimakon ranar 17 ga watan Yuni da aka tsara a baya.

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ne ya kaddamar da taron a wani matakin lalubo hanyoyin magance matsalolin da ke addabar kasar.

A waje daya kuma wakilan taron, sun amince da matsaya kan dokar nan da aka yi ta cece kuce a kanta da ke cikin kundin tsarin mulki wacce ta bai wa gwamnatin Tarayya iko a kan arzikin kasar.

A baya dai wasu wakilai da suka fito daga jihohin da ke da arzikin mai sun nemi a sauya dokar ta yadda jihohin za su sami iko da arzikin kacokan saboda suke ikirarin samarwa kasar.

Karin bayani