Hukumar IMF za ta bai wa Ukraine Bashi

Shugabar Asusun IMF Christine Lagarde Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugabar Asusun IMF Christine Lagarde

Asusun bada lamunai na duniya IMF ya amince yarjejeniyar baiwa kasar Ukraine bashin dala biliyan 17 na tsawon shekaru biyu.

Bashin da aka yi alkawarin ba ta tun a cikin watan Mayu, ya dogara ne ga sharuddan garanbawul ga tattalin arziki da suka hada da kara kudaden haraji, farashin makamashi, da tsayar da yawan mafi karancin albashi .

Kimanin sama da dala miliyan dubu uku ne za a baiwa gwamnatin Ukraine lakadan , wacce ke fuskantar matsin tattalin arziki da rikicin siyasa.

Shugabar Asusun bada lamunin IMF Christine Lagarde ta shaidawa taron manema labarai cewa za a samar da bashin ne hara na tsawon shekaru biyu.

Ms Lagarde ta kuma ce hukumar ta IMF za ta rika sa idon a kai a kai don tabbatar da cewa gwamnatin Ukraine ta cika alkawarin da ta dauka bisa yarjejeniyar.

A baya dai wani babban taron kasa da kasa a birnin London da yanke shawarar tallafawa Ukraine wajen farfado da dubban biliyoyin dalolin da suka kai darajar kadarorin da ake zargin hambararren shugaban kasar Viktor Yanukovich da aminansa sun sace.