An kashe mutane 19 a harin Nyanya

Harin bam a Abuja Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Nigeria na korafi a kan cewar gwamnati ta gaza

Hukumar bada agajin gaggawa ta birnin tarayyar Najeriya Abuja ta ce mutane 19 suka rasu, yayinda 60 suka samu raunuka a harin Nyanya.

Bam din ya tashi a daren jiya a tashar mota ta Nyanya da ke wajen birnin Abuja a kusa da wurin da a cikin makonnin baya aka kai harin bam da ya halaka mutane sama da saba'in.

Hukumomin sun ce har yanzu suna ci gaba da tantance yawan adadin wadanda harin ya rutsa da su dake asibitoci daban-daban a Abuja.

Tun a jiyan jami'an tsaro da suka hada da jami'an ba da agajin gaggawa suka garzaya wurin inda suka kwashe mutanen da abin ya rutsa da su.

Mazauna unguwar suna cewa, abinda ya fashe din ya girgiza gidajen unguwar, kuma mutane sun kidime sosai.