Kerry ya tattauna da Salva Kiir

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kerry ya ce nan bada jimawa ba Salva Kiir zai gana da Riek Machar

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ya ce Shugaban Sudan ta Kudu ya amince da tattaunawar zaman lafiya don kawo karshen rikici a kasar.

John Kerry ya ce watakila za a gana tsakanin Shugaba Salva Kirr da tsohon mataimakinsa, Riek Machar, nan da mako mai zuwa.

Kerry ya ce "Na shaidawa Shugaba Salva Kirr, cewar zabin da suke dashi shine su tattauna don kawo karshen rikicin".

Mr Kerry na magana ne bayan tattaunawa tare da Shugaban a Juba babban birnin kasar, yana dai fatan shawo kan kungiyar tarayyar Afrika ta tura dubban dakaru zuwa Sudan ta Kudu domin dakatar da rikici, wanda galibinsa ake yi saboda kabilanci.