Bama-bamai sun fashe a Kenya

Hukumomin kasar Kenya sun ce akalla mutane ukke ne suka mutu bayan wasu abubuwa sun fashe a birnin Mombasa.

Lamarin ya kuma jikkata wasu dadama.

Hukumomi sun kuma ce mutanen sun mutu ne a wata bus inda aka samu fashewar farkon.

An samu fashewa ta biyun ne a kusa da wani wani babban otel a gabar tekun birnin.

.