Bama-bamai sun tashi a Maiduguri

Jami'an Soji a Maiduguri Jihar Borno Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jami'an Soji a Maiduguri Jihar Borno

Rahotannin daga Maiduguri a jihar Borno arewacin Najeriya na cewa an ji tashin bama-bamai da karan harbe-harbe da tsakar daren jiya

Amma wasu daliban jami'ar Maiduguri sun ce sun ji karan fashewar kusa da su, inda karan harbe-harbe suka biyo baya.

Sun kuma ce an hangi jami'an soji na wucewa ta cikin wani daji dake gefen jami'ar Maidugurin.

Daliban dai na cewa hakan ya haifar musu da fargaba yayin da suke tsakiyar karatun jarabawa a daren jiyan.

Ya zuwa yanzu dai ba a samu labarin ko a ina ne bam din ya tashi ba.