Jonathan zai yi jawabi kan batun tsaro

Hakkin mallakar hoto Getty

An bada sanarwar cewa Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan zai yi wa jama'ar kasar jawabi ranar Lahadi, bayan sukar da gwamnatinsa ta sha a kan yadda ta gaza shawo kan matsalar ta'addanci a kasar.

Ana sukar gwamnatin sosai, musamman ma kan yadda ta kasa warware matsalar sace wasu 'yan mata sama da 200 da aka yi a makarantar sakandare ta Chibok a Jihar Borno.

Ga kuma batun kai hare-haren bama-bamai a Abuja, babban birnin kasar, inda aka kashe fiye da mutane 90 a cikin 'yan kwanakin nan.

Amurka ta ce za ta taimaka wa Najeriyar wajen gano daliban Chibok din da aka sace.

Sakataren harkokin wajen Amurkar, John Kerry, ya ce sace daruruwan yaran da 'yan Boko Haram su ka yi wani rashin imani ne.

Ya ce: "Za mu yi duk abin da ya dace don taimaka wa gwamnatin Najeriya wajen mai da 'yan matan gida."

Karin bayani