Sojoji sun kai samame a Abuja

Hakkin mallakar hoto AFP

Rundunar sojin Najeriya ta ce jami'an tsaro sun kama mutane takwas a Abuja a wani samame da suka kai a unguwar Kugbo da Nyanya.

An samu fashewar bama-bamai a unguwar Nyaya har so biyu a makonni biyu inda mutane dadam suk mutu.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta kuma ce dakarun kasa-da-kasa sun kama wani dan kasar Chadi, wanda ta yi zargin cewa yana aiki da wadanda ta kira 'yan ta'adda.