Tsaro: Za a rufe makarantu a Abuja

Hakkin mallakar hoto AFP

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bada umurnin a rufe dukkan makarantu da kuma ofisoshin gwamnati a babban birnin kasar, Abuja, a tsawon kwanaki ukkun da za a yi ana gudanar da taron tattalin arzikin duniya a makon gobe.

Hukumomin kasar dai sun ce sun dauki matakin ne saboda a kaucewa cunkoson motoci.

An samu fashewar bama-bamai a birnin na Abuja har sau biyu a cikin makonni biyu -- lamarin da yayi ajalin kusan mutane 90.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce Amurka za ta taimaka wa Najeriyar wajen kubutadda sama da 'yan mata 200 da 'yan bindiga suka sace a garin Chibok kusan makonnin ukkun da suka wuce.

Karin bayani