Mutane sama da 30 aka kashe a Ukraine

Rikici a birnin Odessa kasar Ukraine Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rikici a birnin Odessa kasar Ukraine

Mutane fiye da 30 ne aka kashe a wata arangama tsakanin magoya bayan Rasha da na gwamnati a birinin Odessa dake kudu maso yammacin kasar.

Rahotanni sun ce duka bangarorin sun yi ta jefa bama-baman da aka hada da petur da ya haddasa tashin wuta a ginin kungiyiyoyin ma'aikata.

Dama dai tuni mayakan sa kan suka mamaye ginin suka kuma rika harbi kan taron jama'a ta saman rufin kwano.

Mataimakin Ministan harkokin wajen kasar Ukraine Danylo Lubkivsky ya shaidawa BBC cewa ba tare da yin la'akari da ko su wa aka kashe ba, mutuwar mutanen abin bakin ciki ne.

Mr Lubkivsky ya bukaci mahukuntan kasar Rasha yake zargi da kitsa tashin hankalin da su dakatar da duk wasu abubuwan da ka iya yi zagon kasa ga ci gaban yankin.

Gwamnatin Ukraine din ta kuma ce an kashe sojoji biyu a harin da aka kai a shingen binciken ababan hawa dake wajen birin Sloviansk dake kudu maso gabashin kasar.