An kai hari a kasuwa a Jihar Borno

Hakkin mallakar hoto AP

Rahotanni daga Najeriya sun ce wasu 'yan bindiga sun ka hari a wata kasuwa a Jihar Borno dake arewacin kasar.

Mazauna wurin sun ce 'yan bindigar, wadanda ake zaton 'yan Boko Haram ne, sun shiga cikin kasuwar Kayamla dake kusa da Maiduguri, su ka yi ta harbin mutane.

Babu cikakken bayanin irin asarar da aka yi, amma ance an harbi mutane da dama kuma an kone motoci da yawa.

Wani wanda ya ji lokacin da aka kai harin ya ce a yau Lahadi ne da rana 'yan bindigar su ka shiga kasuwar, su ka yi ta harbe-harbe.

Ya ce: "'Yan bindigar sun shiga cikin kasuwar ne su ka yi ta harbin mutane. Sun harbi direban mu ma, wanda yanzu ya na nan rai a hannu-Allah."

Jami'an tsaro dai ba su ce komai ba akan lamarin.

Karin bayani