Iyayen dalibai na cigaba da nuna damuwa

Wasu iyaye a garin Chibok Hakkin mallakar hoto
Image caption Wasu iyaye a garin Chibok

Iyayen dalibai mata fiye da dari biyu da aka sace a Najeriya sun bayyana takaicinsu na jiran gawon shanun labarin halin da 'ya'yansu ke ciki.

Mahaifiyar daya daga cikin 'yan matan mai suna Martha Yarama Ndirpaya ta zargi gwamnatin kasar da kin bayyana gaskiya da taimakawa wajen gano 'ya'yan su;

Tace karya suke fada,sun ce sun gano 'yan mata 120,sai daga baya muka gano cewa karya suke yi,har yanzu babu abinda suka yi.

A karon farko Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi wa al'umar kasar jawabi game da sace yaran ta re da alkawarin cewa za su yi iyakar kokarinsu wajen ganin an ceto yaran.

Sai dai ya amince cewa duk da nemansu da dakarun sojin kasar su ka yi, hakansu bai cimma ruwa wajen gano su ba.