An sako shugabar 'yan Chibok ta Abuja

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Abuja

An sako jagorar da ta shugabanci zanga-zangar bukatar gwamnatin Nigeria ta kara azama domin ceto 'yan matan Chibok su fiye da 200 da 'yan Boko Haram suka sace fiye da makonni uku da suka wuce.

An sako Mrs Naomi Mutah ne wacce aka tsare bisa umarnin uwargidan shugaban Nigeria, Patience Goodluck.

Uwargidan shugaban kasar ta fusata ne, cewa iyayen 'yan matan da aka sace din basu halarci ganawar da ta kira ba, a maimakon haka sai suka tura Mrs Naomi Mutah ta wakilce su.

A ranar Lahadi, Shugaba Goodluck Jonathan ya yi jawabi ga 'yan Nigeria inda ya ce gwamnatinsa na kokari wajen ceto 'yan matan.

A waje daya kuma iyayen 'yan matan da aka sace sun bayyana takaicinsu na rashin samun takamammen bayani daga wajen hukumomin Nigeria a kan makomar 'ya'yansu.

Inda suka ce jawabin Shugaban kasar, bai warware fargabar da suke ciki ba.

Karin bayani