Ana tsare da shugabar al'ummar Chibok

Image caption Daga bisani an dauke Mrs. Naomi daga caji ofis din Asokoro zuwa wani gurin da ba a bayyana ba

Rahotanni daga Abuja na cewa, an tsare shugabar al'ummar Chibok Mrs Naomi Mutah, bayan tattaunawarta da Uwargidan Shugaban kasa, Mrs Patience Jonathan.

Mrs Naomi Mutah wacce ta jagoranci zanga-zangar mata a Abuja, domin matsin lamba ga gwamnati a ceto 'yan mata dalibai fiye da 200, na tsare ne a caji ofis na Asokoro.

Bayanai sun nuna cewa 'yan sanda kuma sun gayyaci kwamishiniyar harkokin mata ta jihar Borno, amma sun sallame ta bayan an yi mata tambayoyi.

Rahotanni kuma sun bayanna cewa Mrs Patience Jonathan ta gargadi matan su daina zanga-zanga ko kuma a dauki mataki a kansu.

Daruruwan mata ne suka yi zanga-zanga a Abuja, babban birnin Nigeria a makon da ya wuce, kan batun sace dalibai 'yan mata a Chibok da ke jihar Borno.

Karin bayani