An sace 'yan kasar Holland uku a Bayelsa

Hakkin mallakar hoto BBC TWO
Image caption Tsagerun Niger Delta

An yi garkuwa da wasu 'yan kasar Holland uku a yankin Niger Delta mai arziki mai a Nigeria a kan hanyarsu ta zuwa duba aikin wani asibiti a jihar Bayelsa.

Kakakin rundunar tsaro a Niger Delta, Mustapha Anka wanda ya tabbatar da hakan ya ce biyu daga cikin mutanen da aka sace maza ne sannan akwai mace daya a cikinsu.

Hukumomi sun ce kawo yanzu ba a san kungiyar da ta sace mutannen ba kuma babu bayani game da ko suna bukar a biya su kudin fansa.

Yin garkuwa da 'yan kasashen waje a yankin Niger Delta wani abu ne da ya zama tamkar sana'a tsakanin matasa a yankin, saboda kudin fansa da ake biya.

An dade ana fama da rikici a yankin Niger Delta kafin gwamnatin Nigeria ta yi wa tsagerun yankin afuwa a shekara ta 2009.