An gano maganin maida tsohuwa yarinya

Bera
Image caption An dai gano maganin tada komadar ne a jikin matasan kananan beraye.

Masu binciken kimiyya a Amurka, sun ce watan watarana za a iya samar da maganin maida tsohuwa yarinya ko maganin hana tsufa.

Hakan ya biyo bayan wasu gwaje-gwaje da aka yi a kan beraye, inda aka sanya wa tsofaffin beraye jinin yaran beraye.

Masana kimiyyar sun ce sun gano cewa yanayin tsufan berayen da aka sanya wa jinin yaran beratuen ya ragu.

Masanan sun kuma ce, za a gudanar da irin wannan gwajin a jikin bil'adama.