Malema nada farin jini a Afrika ta Kudu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Malema a wajen gangamin yakin neman zabe

Dumbin yara dalibai sanye da tufafin makaranta launin fari da shudi suna kada ganguna yayin raka ayarin motocin Julius Malema a kan wata hanyar burji da ta nufi cikin garin Itirteleng da ke cikin halin kunci a kan yankin tuddai na wajen Pretoria.

Cikin dan kankanin lokaci, farin ciki ya sake lullube taron mutane, kimanin 500 da suka yi cincirindo a wani filin wasa mai cike da kura, ga kuma zafin rana don sauraron wannan dan siyasa mai yawan janyo ka-ce-na-ce da cika baki a Afirka ta kudu yayin gangamin yakin neman zabensa.

Mr. Malema mai shekaru 33 wanda ya saba shiga kanun labarai a jaridun yanki, jigo ne da ya yi fice wajen janyo takaddama da cece-ku-ce, ga wasu mutane Malema sha-ka-tafin dan siyasa ne da kafofin yada labarai ke yi wa ingiza mai kantu ruwa, wanda nan gaba kadan zai fuskanci kuliya.

Wasu kuma suna nuna fargaba da wannan dan tabargaza mai goyon bayan akidojin cin gaban rayuwar al'umma da ke fafutukar dabbaka tsarin tattalin arziki irin na Shugaba Mugabe na Zimbabwe, da ke barazanar tarwatsa Afirka ta kudu.

Yayin da mafi yawan mutane ke kallonsa a matsayin daya daga cikin 'yan siyasa mafi kaifin baki wajen sukar dukkan wani aiki na ba daidai ba, da ke neman tagayyara kasar shekaru ashirin bayan maida ita kan tsarin demokradiyya.

'Barkwanci'

A yau, Mr Malema da ke fuskantar tuhuma kan aikata zamba da zarge-zargen tafka badakala da kuma karayar arziki sakamakon wani bincike kan batun haraji, yana sanye da wandon jeans da ya saba bayyana a cikinsa mai lakabin mutum-na-mutane da rigarsa 'yar kantin Burberry da wani kodadden takalminsa gami da hular nan tasa da aka fi sani da taksi direba.

Ko da yake Shugaban kasar mai ci Jacob Zuma, mutum ne da ke iya kayatar da taro ta hanyar iya rawa da rera waka gami da raharsa ta mutanen Zulu, sai dai babu mutumin da ya kama kafar Mr. Malema wajen iya barkwanci da kurari a yayin jawabi.

Image caption Lokacin da ya bayyana gaban kotu

A jawabinsa na tsawon sa'a guda, Malema cikin ba'a ya kalubalanci Shugaba Zuma kan batun miliyoyin kudaden jama'a da ya kashe wajen gyara gidansa, ya ce Nelson Mandela zai yi ta birgima a cikin kabari idan ya ji yadda jam'iyyarsa ta ANC mai mulki ta zama.

Ga kuma yadda ayarin wasu gurbatattun 'yan boko su kalilan ke ci da gumin bakaken fata masu rinjaye da suka yi fama da matsalar wariya.

A cikin barkwanci da shagube, Malema ya yi abin da ya saba kuma ya fi kwarewa a kai wato alkawura- na samar wa al'ummar yankin ruwan sha da ingantattun bandakuna da kuma ninka tallafin kudade don kyautata rayuwar jama'a.

Dandalin ya rude da tafi lokacin da Malema ya ce, "Dole ku farkar da jam'iyyar ANC daga barci. Yanzu lokacinku ne bakaken fata. Samun 'yanci ba tare da 'yancin tattalin arziki ba, ba cikakken yanci ba ne".

Daya daga cikin wadanda suka halarci gangami, Millicent Tsategi ta ce tun da ya yi mana kyawawan alkawura, zai samar mana da ayyukan raya kasa da suka hadar da ruwan sha da ingantattun bandakuna da kuma gidaje, ba shakka za mu ba shi dama.

Karin bayani