Zan ragargaza kungiyar 'yan uwa musulmi - Al-Sisi

Abdulfateh Al Sisi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Abdulfateh Al Sisi shugaban kasar Masar

Mutumin da ake ganin shi ne zai lashe zaben shugaban kasa a Masar, Abdel Fattah Al-sisi ya ce zai sau biyu ana yunkurin kashe shi.

Sai dai ya ce ko kadan hakan bai bashi tsoro ba kuma shi mutum ne da ya yarda da kaddara, Ko da yake bai yi karin haske akan yadda aka so kashe shi ba.

Haka kuma tsohon ministan tsaro na kasar ya ce zai ragargaza kungiyar ta 'yan uwa musulmi idan ya yi nasara a zabe.

Ya kuma kara da cewa babu batun sasantawa da kungiyar 'yan uwa musulmi ta kasar da aka haramta.