Amurka za ta taimaka ga neman 'yan matan Chibok

John Kerry, Sakataren harkokin wajen Amurka Hakkin mallakar hoto AP
Image caption John Kerry, Sakataren harkokin wajen Amurka

Amurka ta bayyana cewar za ta aike da wata tawagar kwararru zuwa Najeriya domin taimakawa ga gano yanmatan makarantar nan fiye da dari biyu da yan Boko Haram suka sace a watan da ya wuce.

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya ce sakamakon amincewar da Shugaban Najeriyar Goodluck Jonathan yayi da tayin, ofishin jakadancin Amurka a Abuja na kafa wani kwamitin tsare tsare.

Zai hada da jami'an sojin Amurka da sauran jami'an tsaro da kuma masu sasanta cetar wadanda aka yi garkuwa da su.

A waje daya kuma 'yan bindiga da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun sace karin wasu 'yan mata takwas a wani kauye da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Nigeria.

An sace 'yan matan ne a kauyen Warabe da ke kusa da Gwoza a ranar Lahadi da daddare, inda 'yan Boko Haram din suka arce da su a cikin motoci irin na jami'an tsaro.

Mazauna garin sun ce, 'yan Boko Haram din da dama ne suka aukawa garin dauke da manyan makamai.

Rahotanni sun ce 'yan kungiyar sun kwashi hatsi daga shaguna sannan kuma suka yi harbe-harbe.

Hakan na zuwa ne bayan da 'yan Boko Haram din suka sace 'yan mata dalibai kusan 200 a garin Chibok da ke jihar ta Borno.

Kasashe da kungiyoyi da dama sun yi tayin agaza wa Najeriyar don shawo kan rikicin na Boko Haram.

'Takaici'

A sassa da dama na Nigeria, ana ci gaba da nuna kaduwa da kuma takaici kan faifan bidiyon da kungiyar Boko Haram ta fitar a ranar Litinin.

Image caption 'Yan mata 53 sun kubuce daga hannun 'yan Boko Haram

An dai nuna jagoran kungiyar ne, Abubakar Shekau, yana tsaye a gaban wasu motocin yaki masu sulke, yana cewar kungiyarsu ce ta sace daliban nan 'yan mata su sama da dari biyu, makonni uku da uka wuce, ya kuma ce suna da niyyar sayar da su.

'Yan Nigeria da dama na mamakin yadda 'yan kungiyar ke ci gaba da cin karensu ba tare da babbaka ba, da kuma yadda sojoji suka gaza gano wadannan 'yanmata.

Gwamnatin kasar ta ce tana kokarin ceto 'yan matan.

Ministar kudin kasar Mrs Ngozi Okonjo-Iweala ta ce " A cikin makonni ukun da suka wuce, gwamnati na bin dukkan wasu bayanai da ta samu, da amfani da jiragen sama, da da sauran dabaru, domin gano wadannan 'yan mata".

Karin bayani