An sace motar 'yan makaranta a Nyanya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dalibai a Nigeria na fuskantar barazana daga wajen Boko Haram

Rahotanni daga Nyanya da ke wajen garin Abuja a Nigeria na cewa wasu 'yan bindiga sun sace motar wata makaranta.

Rahotannin sun kuma ce 'yan bindigar sun sace yara uku a motar makarantar ta Vine international da ke Nyanya a ranar Talata.

Sai dai wata jami'a a makarantar ta musanta cewa an sace yaran.

Jami'ar ta ce 'yan bindigar sun bukaci direban motar da ya basu mukullin motar ne, sannan suka yi awon gaba da ita.

Ita ma mai magana da yawun rundunar 'yan sandan birnin Abuja Altine Daniel, ta shaida wa BBC cewa ya zuwa yanzu bincikensu ya nuna cewa motar makarantar kadai aka sace.

Ta kuma ce 'yan sanda sun isa makarantar, domin gudanar da bincike game da batun.

Sau biyu dai ana kai harin bama-bamai a Nyanya wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 100.