An yi zabe a Afrika ta Kudu

Masu zabe a Afrika ta Kudu Hakkin mallakar hoto
Image caption Masu zabe a Afrika ta Kudu

'Yan Afrika ta Kudu masu dimbin yawa ne suka fita domin kada kuri'unsu a babban zaben kasar, yayinda take cika shekaru ashirin da kawo karshen mulkin fararen fata 'yan tsiraru.

An kafa dogayen layuka, kuma mutane na cikin zumudin kada kuri'unsu, musamman ma wadanda ke yin zaben a karon farko, wato wadanda aka haifa a karshen mulkin wariya a 1994.

Ana sa ran jam'iyyar ANC mai Mulki ce zata samu rinjaye da kamar kashi sittin cikin dari, amma yakin neman zaben nata ya ci karo da cikas saboda damuwar da ake nunawa kan karuwar rashin aikin yi da kuma cin hanci da rashawa.