An gargadi Boko Haram kan sayar da 'yan mata

Hakkin mallakar hoto
Image caption Wannan matar an sace mata diyar ta

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewar barazanar 'yan Boko Haram na sayar da 'yan matan da suka sace zai iya zama cin zarafin bil adama.

Kakakin Ofishin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya, Rupert Colville ya ce sun damu matuka a kan barazanar sayar da 'yan matan da 'yan Boko Haram suka sace.

Colville ya ce "Mun yi Allahwadai da wannan batun kuma an haramta matakin mayar da mutane bayi a karkashin dokar kasa da kasa".

A sassa da dama na Nigeria, ana ci gaba da nuna kaduwa da kuma takaici kan faifan bidiyon da kungiyar Boko Haram ta fitar a ranar Litinin.

An dai nuna jagoran kungiyar ne, Abubakar Shekau, yana tsaye a gaban wasu motocin yaki masu sulke, yana cewar kungiyarsu ce ta sace daliban nan 'yan mata su sama da dari biyu, makonni uku da uka wuce, ya kuma ce suna da niyyar sayar da su.

'Yan Nigeria da dama na mamakin yadda 'yan kungiyar ke ci gaba da cin karensu ba tare da babbaka ba, da kuma yadda sojoji suka gaza gano wadannan 'yanmata.

Gwamnatin kasar ta ce tana kokarin ceto 'yan matan.