Anya za a iya ceto 'yan matan Chibok ?

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Iyayen 'yan matan na cikin damuwa

Kungiyar Boko Haram ta sace 'yan mata 276 a wata makarantar sakandare ta kwana da ke Chibok a jihar Borno a ranar 14 ga watan Afrilu.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Bayanai sun nuna cewar 'yan Boko Haram kusan 200 ne suka kai hari a cikin dare a garin inda suka kutsa cikin makarantar sannan kuma suka arce da daliban tare da sace kayayyakin abinci.

Me yasa aka sace 'yan matan?

Kungiyar Boko Haram na adawa da karatun Boko kuma ta bukaci 'yan mata su bar makaranta su je su yi aure.

A baya sun kai hare-hare a kan makarantu abinda ya sa aka rufe sauran makarantu kenan a jihohin arewa maso gabashin Nigeria.

An bar makarantar Chibok ta 'yan mata a bude ne saboda dalibai su rubuta jarabawar karshe ta kamalla karatun sakandare kuma babu jami'an tsaro da ke kare lafiyarsu.

Shin 'yan Boko Haram sun taba sace 'yan mata?

Hakkin mallakar hoto Reuters

A lokacin da 'yan Boko Haram suka kai hari a wata makaranta a jihar Yobe a watan Maris, sun kashe dalibai maza 29 amma ba su taba 'yan mata ba. Inda suka umurce su su koma gida su yi aure.

Masu sharhi na gannin cewar daliban ba su ji umurnin Boko Haram ba, abinda ya sa suka sace 'yan matan Chibok kenan.

Sai dai a wani bidiyo a cikin watan Mayu, Abubakar Shekau ya ce su ne suka sace 'yan matan Chibok kuma ya yi barazanar sayar da su.

Shin 'yan Boko Haram sun taba sakin mutanen da suka sace ?

Hakkin mallakar hoto Reuters

Wani kwararre kan tsaro a Amurka, Jacob Zenn ya ce a wasu lokuta ana bani gishiri in baka manda, inda jami'an tsaro ke musayar fursunoni da 'yan Boko Haram.

A watan Fabairun 2013, 'yan Boko Haram sun sace wasu Faransawa bakwai a Kamaru, amma daga bisani sun sake su.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce an biya kudin fansa kusan dala miliyan uku kafin a sako Faransawan.

Amma gwamnatocin Faransa da Kamaru sun musanta.

A cikin watan Junairun bana, sun kama malamin coci Georges Vandenbeush amma an soke shi bayan makonni bakwai. Anan ma Faransa ta musanta biyan kudin fansa.

Ta yaya za a gano adadin 'yan matan da aka sace ?

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan mata da suka kubuce daga hannun Boko Haram

'Yan mata hamsin da takwas sun kubuce, wasunsu sun dira daga cikin motoci ne a lokacin da ake tafiya da su.

Kamfanin dillancin labarai na AP ya ce wani mai shiga tsakani na tattaunawa da 'yan Boko Haram.

A cewar AP din biyu daga cikin 'yan matan sun mutu sakamakon cizon maciji a yayinda 11 suke fama da rashin lafiya.

Hukumomi sun ce watakila wasu 'yan matan sun kubuta amma kuma iyayensu sun ki fadi.

Ta yaya 'yan Nigeria suka maida martani?

Hakkin mallakar hoto Reuters

'Yan Nigeria na cike da takaici game da yadda batun yaki ci yaki cinyewa.

An gudanar da zanga-zanga a jihohin kasar da dama don matsawa gwamnati lamba don ta tashi tsaye ta gano inda 'yan matan suke sannan ta kubutar da su.

Shugaban kasar, Goodluck Jonathan ya ce gwamnatinsa na kokarin ceto 'yan matan.

Haka kuma rundunar 'yan sandan Nigeria ta sanarda ba da tukwicin naira miliyan hamsin ga duk wanda ya taimaka da bayanai kan yadda za a gano da kuma ceto 'yan mata dalibai da aka sace a Chibok.

Hakkin mallakar hoto AFP

A cikin wata sanarwa, kakakin rundunar CSP Frank Mba ya ce duk wanda ya bada bayanai, za a yi amfani da bayanan a cikin sirri ba tare da al'umma sun sani ba.

Karin bayani