Barkewar cutar kwalera a jihar Plato

Kwayar cutar kwalera Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Kwayar cutar Kwalera

Rahotanni daga jihar Filato a Nijeriya na cewa cutar amai da gudawa ta barke a wasu kananan hukumomi inda ake samun hasarar rayuka.

Cutar dai ta barke ne a Barikin ladi da Jos ta kudu, da Jos ta arewa da kuma Basa.

Wani magidancin ya shedawa BBC cewa iyalinsa biyu su sun kamu da cutar .

Hukumar samar da agaji cikin gaggawa ta jihar ta ce ta soma daukar matakan shawo kan matsalar .