'An kashe mutane da dama a Gamboru Ngala'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau

Rahotanni daga garin Gamboru Ngala na jihar Borno da ke makwabtaka da Kamaru sun ce mutanen da aka kashe sun kai 600 a harin da 'yan Boko Haram suka kai a ranar Litinin.

Wata 'yar garin ta shaidawa BBC cewar sun shafe yinin ranar Laraba suna jana'izar mutanen da aka kashe, inda ta ce ana saka mutane 10 cikin kowanne kabari.

Matar wacce bata son a fadi sunanta ta ce " An kona kasuwarmu kurmus, an kona motoci 410 sannan mutane kusan 600 aka kashe".

A cewarta a yanzu ana cikin yanayi na yunwa a garin na Gamboru Ngala sakamakon ta'adin da 'yan Boko Haram suka yi.

Dama dai Sanata Ahmed Zanna dan majalisar dattijai daga jihar Borno ya shaida BBC cewar mutane kusan 300 aka kashe a garin na Gamboru Ngala a harin na ranar Litinin.

'Yan kungiyar Boko Haram na tafka ta'asa a yankunan arewa maso gabashin Nigeria, inda suka hallaka dubban mutane daga farkon wannan shekarar zuwa yanzu.

Karin bayani