Chibok: Amurka ta tura dakaru Nigeria

Jagoran kungiyar boko haram Abubakar Shekau Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Jagoran kungiyar boko haram Abubakar Shekau

Amurka ta tura wata tawaga da ta kunshi kwararru a kan tsaro zuwa Najeriya, wadanda zasu taimaka wajen neman 'yan matan Chibok.

A hirar da ya yi da wata kafar talabijin a Amurka, shugaba Obama ya ce tawagar ta kunshi sojoji da jami'an tsaro da kuma jami'an wasu hukomoni wadanda zasu yi kokarin gano takamaimai wurin da aka ajiye 'yan matan.

Shugaba Obama ya bayyana 'yan matan da kungiyar boko haram ta sace, a matsayin abin tausayi da kuma takaici, yana mai yin tur da al'amarin.

Sai dai ya ce watakila lamarin ya sa kasashen duniya su farga wajen aiki tare, domin daukar mataki a kan kungiyar ta Boko Haram

Jami'an Amurka sun ce watakila an wuce da wasu daga cikin 'yan mata zuwa kasashen Chadi da kuma Kamaru, dake makwabtaka da Najeriya ko da yake jami'ai a kasashen Chadi da Kamaru sun musanta haka.