Chibok: Za a ba da ladan naira miliyan 50

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jami'an tsaro na kokarin ceto 'yan matan Chibok

Rundunar 'yan sandan Nigeria ta sanar da ba da tukwicin naira miliyan hamsin ga duk wanda ya taimaka da bayanai kan yadda za a gano da kuma ceto 'yan mata dalibai da aka sace a Chibok.

A cikin wata sanarwa, kakakin rundunar CSP Frank Mba ya ce duk wanda ya bada bayanai, za a yi amfani da bayanan a cikin sirri ba tare da al'umma sun sani ba.

Sanarwar kuma ta bukaci 'yan kasar da ke da bayanai, su tuntubi 'yan sanda a lambobin salula guda shida da suka bayar; 09-2914649, 08081777309, 08055547536, 08032125050, 08034617591, 08035969731.

Rundunar 'yan sanda kuma ta bukaci al'ummar kasar su taimaka waje shawo kan kalubalen tsaron da ake fama da shi a kasar.

A ranar 14 ga watan Afrilu ne 'yan Boko Haram suka sace dalibai 'yan mata 276 a makarantar sakandare ta Chibok da ke jihar Borno.

Kwanaki biyu bayan afkuwar lamarin, gwamnan jihar Borno Alhaji Kashim Shettima ya yi tayin bada tukwicin naira miliyan hamsin don gano inda 'yan matan suke amma kawo yanzu ba a gano bakin zaren ba.

Karin bayani