'Yan tawayen Syria sun fice daga Homs

Mayakan 'yan tawayen Syria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wakilin BBC ya ce 'yan tawayen da iyalansu sun fice daga birnin cikin bacin rai

Mayakan 'yan tawaye da iyalansu na ficewa daga birnin Homs, bayan kwashe shekaru ana fafatawa tsakaninsu da dakarun Syria.

Hayaki ya turnuke sararin samaniya a wasu sassan birnin, mazauna birnin sun ce 'yan tawayen sun kona sansanoninsu da kayayyakinsu.

'Yan tawayen na barin birnin ne bayan wata yarjejeniyar da aka cimma da gwamnati, karkashin sa idon Majalisar Dinkin Duniya.

Ficewar 'yan tawayen daga Homs ya kawo karshen tayar da kayar bayan da suke yi a birnin da aka taba bayyanawa a matsayin cibiyar juyinjuya hali.