Za a gudanar da zabe a Africa ta Kudu

Shugaban kasar Africa ta Kudu Jacob Zuma Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Har yanzu da dama daga cikin al'umar kasar na yin biyayya ga jam'iyyar ANC

A yau ne kasar Africa ta kudu za ta gudanar da zabe gama gari, zaben da a cikinsa mutanen da ba su taba sanin menene mulkin wariyar launin fata ba saboda shekarunsu amma a yanzu su na da 'yancin kada kuri'a.

Ana saran gwamantin jam'iyyar African National Congress wato ANC za ta lashe zaben da gagarumin rinjaye duk da zargin cin hanci da rashawa da kuma tafiyar da dukiyar kasa ba bisa ka'ida ba da ake mata.

Wakilin BBC a birnin Johannesburg ya ce shekaru ashirin kenan amma har yanzu da dama daga cikin al'umar Africa ta Kudu na yin biyayya ga jam'iyyar ANC.

Saboda ta samar da zaman lafiya da gidaje masu sauki ga talakawa da kula da walwalar jama'a.

Haka kuma watakil mutuwar tsohon shugaban kasar Nelson Mandela a watannin da suka gabata ya karawa jam'iyyar magoya baya.