An aikata laifukan yaki a Sudan ta Kudu

Wadanda rikicin Sudan ta Kudu ya rutsa da su Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dubban mutane ne dai rikicin ya rutsa da su, wasu sun rasa rayukansu ya yin da wasu suka bar matsugunansu.

Wani rahoto da hukumar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta fitar ta zargi dukkan bangarorin da ke rikici da juna a Sudan ta Kudu da aikata laifukan yaki da cin zarafin bil'adama.

Rahoton ya dogara ne da shaidu wadanda suka gani da idanunsu da kuma wadanda abin ya shafa suka bayar, da ya yi kiyasin cewa an kashe dubban maza da mata da kananan yara wadanya yawanci an yi su ne akan rikicin kabilanci.

An kuma bayyana yadda aka ci rafin mata ta hanyar yi musu fyade, da gidadjen da aka kona a garuruwa da kauyuka da kuma sace-sace.

Ana sa ran Shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir da shugaban 'yan tawaye kuma tsohon mataimakinsa Riek Mashar za su yi tattaunawar sulhu a gobe juma'a dan kawo karshen rikicin.

Haka kuma nan gaba a yau ne MDD za ta wallafa nata rahoton na cin zarafin bi'adama a lokacin yakin.