Barclays zai sallami ma'aikata 19,000

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Barclays nada rassa da dama a duniya

Shahararren bankin Barclays na Birtaniya ya ce zai sallami ma'aikata 19,000 daga nan zuwa karshen shekarar 2016.

Daga cikin sauyin da ya gabatar, ma'aikata 9,000 ne bankin zai sallama a Birtaniya ka dai.

Bankin na Barclays na matsala sakamakon rashin karbar bashi daga wajen gwamnati da kuma kamfanoni

Bankin kuma zai fitar da wani tsari ta hanyar takardun lamuni don sayar da wani bangare na bashin fan biliyan 115 da yake bi.

Zai kuma hada da kadarorinsa da kudin su ya kai fam biliyan 90 da sauran harkokin sa na bankin kananan 'yan kasuwa da ke Turai da suma kudin su ya kai fam biliyan 16 domin rage bashin.

Barclays din zai rage harkokinsa a kasashen Spain da Portugal da Italiya da Faransa.

A cewar shugaban bankin, Anthony Jenkins, wannan wani kwakkwaran mataki ne na saukakawa bankin.

'Rasa ayyukan yi'

Za a rage mafi yawan ma'aikatan cikin wannan shekarar, inda mutane 14,000 za a sallame su a rassa daban daban na bankin.

Tun da farko adadin da bankin ya bayyana cikin wannan shekara ya zarta daga 10,000 zuwa 12,000.

Kimanin mutane 8,000 'yan kasar Birtaniya ne za a sallama daga cikin mutane 14,000 da bankin zai sallama a wannan shekarar.

Hakanan ana sa ran bankin zai sallami wasu masu rike da manyan mukamai mutum 5,000 a shekarar 2016.

Mai magana da yawun bankin ta ce, bankin ya dauki ma'aikata da yawansu ya kai 26,000.

Bankin Barclays da ke Birtaniya ya na da ma'aikata 32,900 da wasu kusan 5,900 a Nahiyar Turai.

Karin bayani