Takaddama kan #BringBackOurGirls

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Iyayen 'yan matan da aka sace

Ana ta muhawara a shafukan intanet game da wane ne ya fara amfani da sakon twitter mai taken #BringBackOurGirls, wanda ya zuwa yanzu aka aika shi sau miliyan daya da dubu 300. To, aikin wane ne wannan?

Kafar yada labaran Amurka ta ruwaito cewa wata mai shirya fina-finai a Los Angeles, Ramaa Mosley ce ta kirkiro wannan taken twitter bayan ta baza shi a shafinta na @MaryStrawberry.

Wannan ikirari ya harzuka wasu 'yan Nijeriya. Shafin twitter na @cchukudebelu ya ce "wannan ma ai raha ce, 'yan Najeriya ne suka kirkiro wannan take amma ba @MaryStrawberry" ba.

Wani na cewa "kamar yadda 'Oprah Wimprey ta ceto Afirka ta kudu daga mulkin wariya', haka ma @MaryStrawberry 'ta kirkiro taken gangamin a kan 'yan matan da aka sace'. Ko ma dai mene ne.

Ra'ayoyin suna nan birjik." Masu amfani da shafin twitter cikin hanzari ke maida martani da zayyana cewa Mosley ce ta buga wannan take a ranar 26 ga watan Aprilu, kwanaki kalilan bayan fara amfani da shi.

Sai dai wasu na cewa maida hankali a kan wanda ya fara amfani da wannan taken twitter ko hashtag janye hankali ne a kan ainihin matsalar da ake ciki. "kafin ku fara tada jijiyar wuya kan @clancycnn da @marystrawberry, ku tuna cewa lamarin ba na wane ne ya kirkiri take ba ne" a sakon tiwitar Ikenna A. Okonkwo, wani masani kan ilmin halittun karkashin kasa da ke zaune a Nijeriya.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Kamar yadda muka ruwaito a wannan shafi, wani Lauya a Nijeriya, Ibrahim M Abdullahi, shi ne mutum na farko da ya fara aika wannan taken twitter.

Bayan kara bin diddigi, ta bayyana cewa hakika, shi ne na farkon fari. Ya ji tsohuwar ministar ilmi, Obiageli Ezekwesili na jawabi yayin wani taro a birnin Fatakwal na Nijeriya.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

A ranar 23 ga watan Aprilu kuma, sai Ibrahim Abdullahi ya aika sakon twitter a kan kalamanta inda ya yi amfani da taken #BringBackOurGirls. Daga nan sai Ezekwesili ta sake aika sakon Abdullahi.

Karin bayani