Sojin Nigeria: 'Sai mun ceto 'yan Chibok'

Dakarun sojin Nijeriya a fagen aiki Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shalkwatar tsaro ta ce ba ta da wani gilli a kan gangamin a dawo mana da 'ya'yanmu mata

Shalkwatar tsaro ta Nijeriya ta ce sojojin kasar na da karfin ceto 'yan matan Sakandaren Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace.

A cikin wata sanarwa da ta fitar don musanta wasu rahotannin kafofin yada labarai da ke cewa sojojin Nijeriya ba su da karfin ceto 'yan matan, shalkwatar ta ce abin takaici ne yadda wasu ke kokarin tauye yunkurin ceto 'yan mata da kuma harzuka jama'a kan dakarun soja.

Ta ce dakarun soja ba za su rika musayar yawu da wakilan gangamin "a dawo mana da 'ya'yanmu mata ba". Kuma babu wani yunkuri daga wani mutum ko kungiya da zai yi nasarar tsoma sojoji cikin siyasa, yayin da suka dukufa ga aikin ceto 'yan matan da aka sace.

Shalkwatar ta bai wa 'yan Nijeriya tabbacin cewa duk da kudurin wasu mutane da ke son yin kafar ungulu ga dakarun soja, za ta ci gaba da aikin murkushe yan tada-kayar-baya a yankin arewa maso gabas da shawo kan matsalolin tsaro a fadin kasar.