Chibok: Malala na son duniya ta sa kaimi

Malala ta yi jinya a asibiti a Ingila Hakkin mallakar hoto University Hospitals Birmingham NHS Foundation Trust

'Yar Pakistan din nan da kungiyar Taliban ta kai wa hari, Malala Yousafzai ta ce ya zama dole duniya ta tashi tsaye kan batun sace 'yan matan Chibok.

Malala ta shaida wa BBC cewa "Idan muka kawar da kai, lamarin zai bazu kuma zai yi ta faruwa".

Kungiyar Boko Haram ce ta sace 'yan Matan Chibok 276, sama da makonni uku da suka wuce a jihar Borno, da ke arewa-maso-gabashin Najeriya.

Matashiyar 'yar shekaru 16 ta tsallake rijiya da baya a lokacin da aka harbe ta a kai, a kasar Pakistan a shekarar 2012 a kan gangaminta na bai wa 'ya'ya mata ilimi.

Karin bayani