Kungiyar OIC ta yi tur da satar 'yan Chibok

Sakatare janar na OIC Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Babbar makarantar Islamic Fiqh da ke Saudiyya ta ce ayyukan Boko Haram sun sabawa Musulunci

Manyan Malaman Musulunci na duniya karkashin inuwar kungiyar kasashen musulmi ta OIC, sun yi tur da sace 'yan matan Chibok.

Haka kuma sun yi kira da kungiyar Boko Haram ta saki 'yan matan ba tare da bata lokaci ba.

Hukumar kare hakkin bil'adama ta OIC ta ce, ikirarin Boko Haram na cewa sace 'yan matan da kuma sayar da su daidai ne da dokokin Islama, ba gaskiya ba ne.

Hukumar ta jaddada muhimmancin neman ilimi da cewa muhimmin abu ne a musulunci.