Apple na shirin sayen Beats

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Abin sauraro na Beats na da farin jini a duniya

Rahotanni na bayyana cewa, katafaren kamfani fasahar nan na Apple a yanzu haka yana kan tattaunawa da kamfani samar da kayan latirin watau "Beat" mai kera na'urar jin sauti ta kunne da kuma tura kade-kade ta hanyar waya kan kudi dala biliyan $3.2.

Kamar dai yadda rahotannin suka bayyana, akwai alamun kamfanin na Apple zai iya biyan dala biliyan $3.2 watau fam biliyan (£1.9bn) ana kuma sa ran za a sanar da yadda cinikin ya kaya a maku mai zuwa.

Idan wannan ciniki ya tabbata, zai zamo wata babban ciniki da kamfanin Apple ya taba samu.

Ana kuma kallon wannan yunkuri na Apple a matsayin neman samun gindin zama daram a kasuwar wayoyi da hakimiyar saka kade-kade a wayoyi ta hanyar sadarwa ta intanet.

Haka kuma ana hasashen cewa wadannan bangarori biyu za su samu ci gaba cikin gaggawa nan da wasu shekaru ma su zuwa.

Jaridar Financial Times wacce ita ce ta fara ambata batun cinikin, ta bayyana cewa majiyar na cewa har yanzu kamfanonin na kan tattaunawa.

Wani mai shirya wakoki, Jimmy Iovine da wani shahararren mawaki Dr Dre su ne suka kafa kamfanin Beats har ya kawo lokacin da ya yi fice a wannan bangaren na'ororin hanyar sauraran sauti ta kunne.

A farkon wannan shekarar ne kamfanin ya fara tura wadanda suka biya kudi kade-kade cikin wayoyin su.

Karin bayani