Mutanen Gamboru Ngala na fuskantar yunwa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Maharan sun kuma kona gidaje da dama a Gamborin Ngala

Al'ummar garin Gamboru Ngala da ke jihar Borno a Nigeria na fuskantar barazanar yunwa, saboda karancin abinci da ruwan sha.

Wasu mazauna garin sun ce sai sun tafi zuwa garin Fotokol da ke jamhuriyar Kamaru, kafin su samu abinci.

Hakan ya biyo bayan farmakin da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram suka kai garin a farkon makon nan, inda suka kashe mutane sama da 300, suka kuma kona kasuwar garin, kan suka kwashe musu kayan abinci.

Haka zalika rahotanni sun ce maharan sun kuma karya gadar garin, lamarin da ya hana shigar da kayayyaki cikin garin.

Karin bayani