Tawagar kwararrun Amurka ta isa Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr John Kerry

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya ce tawagar kwararrun Amurka ta isa Nigeria domin taimakawa a kubutar da yan matan Chibok.

Mr Kerry ya ce tawagar za ta yi duk abinda za ta iya tare da gwamnatin Nigeria don maida 'yan matan ga iyayensu da kuma magance barazanar 'yan kungiyar Boko Haram.

Tun farko, Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya ce aikin ta'addanci ne babbar barazanar da kasarsa ke fuskanta.

Sama da makonni uku ke nan har yanzu ba a ji duriyar 'yan matan ba, duk da ikirarin da hukumomin ke yi na kokarin kubutar da su.

An dai soki hukumomin Nigeria kan tafiyar hawainiya wajen maida martani ga satar 'yan matan.

Kungiyar Boko Haram wacce ta sace 'yan matan, ta ce za ta sayar da su a kasuwa.