'Yan Boko Haram sun tarwatsa gada

Hakkin mallakar hoto AFP

Rohotanni daga Najeriya sun ce wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun tarwatsa wata gada a karamar hukumar Gwoza dake Jihar Borno.

Gadar ita ce ta biyu da 'yan bindigar suka rusa jihar a cikin kwanaki biyu.

Ana ganin cewa wannan kamar wata sabuwar dabara ce don kawo cikas ga aikin ceto 'yan matan nan da aka sace daga makarantar sakandare ta Chibok a jihar.

Gadar dai, wadda su ka tarwatsa a jiya, ta hada kauyen Limankara dake cikin Karamar Hukumar ta Gwoza da garin Michika dake Jihar Adamawa.

'Yan bindigar dai sun kai wa kauyen Limankaran hari inda su ka kona gidaje da dama da kuma shaguna, inji mazauna kauyen.

Ba a samu rahoton asarar rayuka ba a harin saboda mazuna kauyen sun tsere bayan sun samu labarin cewa za a kai masu harin.

Karin bayani