Ana zaben shugaban kasa a Lithuania

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Akwai 'yan takara shida da ke hamayya da shugaba Dalia Grybauskaite

Al'ummar kasar Lithuania na zaben shugaban kasa, inda batun kasancewar Rasha a iyakar kasar ya kankane yakin neman zabe.

Shugabar da ke kan mulki Dalia Grybauskaite na da gagarumin goyon baya a kuriar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar.

Shugabar ta samu wannan tagomashi ne saboda adawar da take nunawa ga mamayar da Rasha ta yi a Crimea.

Da kuma yadda shugabar take kokarin ganin an kara yawan sojojin NATO a Lithuanian.

Sai dai kuma ba a san ko za ta samu gagarumar nasara kai tsaye ba a zagayen farko na zaben idan masu zabe ba su fito sosai ba.