Matar Obama ta la'anci sace dalibai

Hakkin mallakar hoto bbc

Uwar gidan shugaban Amurka Barrack Obama ta bayyana sace daliban Chibok da aka yi da cewa wani rashin imani ne, domin hana 'yan mata cimma burinsu na samun rayuwa mai kyau.

Michelle Obama, wadda tayi jawabi a madadin mai gidanta a jawabin da ya saba yi a duk mako ta rediyo, ta ce abinda ya faru a Najeriya abin takaici ne.

Tace: "Kamar sauran milyoyin mutane a fadin duniya, mijina da ni mun fusata, zuciyarmu kuma ta kadu akan sace 'yan mata 'yan Najeriya fiye da dari biyu daga dakunansu na makaranta a tsakar dare.

"Gungun 'yan ta'adda ne su ka yi wannan aikin rashin imani, domin hana 'yan matan nan samun ilmi.

"To Ina son kusan cewa Barrack ya umurci gwamnatimmu ta yi dukkan abinda ya kamata domin taimaka wa gwamnatin Najeriya a kokarin gano wadannan 'yam mata, a maida su gida."

Amfanin ilmin mata

Michella Obaman ta kuma ce abinda ya faru a Najeriyar wani bangare ne na matsalolin da su ka addabi 'yan mata a duniya, musamman ma na rashin samun ilmi.

"Fiye da 'yam mata milyan 65 a duniya ba a sanya su makaranta ba. Hakan kuwa duk da mun san cewa 'yam matan da suka yi makaranta sun fi samun aiki mai armashi da koshin lafiyarsu da kuma lafiyar iyalinsu," inji ta.

"Haka ma, sanya 'yan mata makarantu sakandare na bunkasa tattalin arzikin kasa baki daya.

"Saboda haka, a gaskiya, ilmi shine abu mafi mahimmanci wajen kyautata makomar yarinya -- ba wai don kanta kawai ba, a'a, har ma don iyalinta da kuma kasarta."

Karin bayani