Afghanistan: Sojojin Birtaniya sun tashi daga Helmand

Kasar Afganistan
Image caption Kasar Afganistan

Sojojin Birtaniya da ke Afghanistan sun tashi daga karamin sansaninsu na karshe da ya rage a lardin Helmand.

Sauran sojin Birtaniyan da suka rage kawai yanzu a lardin, su ne na babban sansaninsu na Camp Bastion, wanda shi ma kuma za su bar shi nan gaba a shekarar nan.

A lokacin tsakar aikinsu, akwai sansanoninsu har 137 a lardin.

Mafi yawan sojin Birtaniya 453 da aka kashe a Afghanistan, an hallaka su ne a aikin da suka yi a Helmand din,wanda suka fara shekaru takwas da suka wuce.

Sakataren tsaron Birtaniya, Philip Hammond, wanda ya ziyarci lardin na Helmand, a kwanakin nan, ya ce kai sojojin yankin ya yi amfani duk da dimbin asarar rayukan da suka yi.