An sanya dokar hana fita a Kachia

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

A Najeriya an sanya dokar hana fita ta awoyi 24 a garin Kachia dake Jihar Kaduna bayan da aka sami wani rikici tsakanin matasa Kiristoci da Musulmi.

Rahotanni sun ce rikicin ya biyo bayan rusa wani bangare na bangon Masallaci Eidi ne na garin, wadda a baya ma an taba rusa shi.

Mazauna garin sun ce wannan ya sanya matasa Musulmi fitowa domin su nuna rashin gamsuwarsu.

A ciki haka ne hatsaniya ta tashi tsakanin bangarorin biyu.

Babu rahoton asarar rayuka a rikicin, amma an kona wasu wuraren Ibada.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Alhaji Umar Usman Shehu, ya bayyana cewa an shawo kan lamarin.

Ya kuma ce an sanya dokar hana fita a garin, an kuma baza 'yan sanda su na sintiri.

Kwamishinan ya kuma gargadi jama'a da guji tayar da hankali.

Yace: "Mutane, don Allah, su yi hakuri da juna. Kowa ya ajiye makamansa, ya koma gidansa, ya zauna lafiya da juna -- kuma a baiwa juna hakuri."

Karin bayani