Chibok: Gwamnati ta kafa cibiyar bayanai

Image caption A ranar Litinin 12 ga watan Mayu Cibiyar za ta fara aiki

Gwamnatin Nigeria ta kafa cibiyar samar da bayanai kan ayyukan da jami'an tsaron kasar ke yi don ceto 'yan matan nan sama da 200 da 'yan Boko Haram suka sace.

Gwamnatin kasar ta ce ta dauki wannan mataki ne don bai wa 'yan kasar da wasu al'ummomi da ke kasashen waje damar samun cikakken bayani kan irin kokarin da jami'an tsaron ke yi na ceto 'yan matan.

Dr Doyin Okupe mai taimaka wa shugaban Najeriya kan harkokin hulda da jama'a ya ce an yi haka ne domin magance sukan da ake yi wa gwamnati cewa ba ta bayar da bayanan da suka kamata.

Karin bayani