Ana kuri'ar raba gardama a Ukraine

Hakkin mallakar hoto AFP

Ana kada kuri'ar raba gardama a gabashin Ukraine wadda magoya bayan Rasha suka shirya.

Mazauna yankunan Donetsk da Luhansk ne ke kada kuri'ar cewa ko su na goyon bayan ballewa daga Ukraine.

Mutane da dama sun yi dogayen layuka domin kada kuri'ar.

Wani mutum mai suna Konstantin ya ce: "Na jefa kuri'ar goyon bayan Donetsk.

"Mi yasa? Saboda ba na farin ciki da gwamnati. Ina fatan ni da iyalina za mu rayu a cikin kasar dake zaune lafiya."

Ita ma Ivanova ta bayyana ra'ayin neman balewa daga Ukraine.

"Ina kaada kuri'ar neman 'yancin Donestk, saboda mun gaji da jin karairayin Kiev.

"Ba mu son zaben shugaban kasa, mu zabi wanda a nan gaba zai rka tunanin hadewa da Rasha."

Sojin sa-kan da suka shirya kuri'ar raba gardaman ne dai za su kirga kuri'ar, su kuma bayyana sakamakon zaben.

Wani mukarabbin shugaban wucin-gadin kasar Ukraine din ya yi Allah-wadai da abin.

Gwamnatocin Yammacin Turai ma sun ce haramtacce ne.

A waje daya kuma rahotanni na nuna cewa an samu karin aringama tsakanin dakarun gwamnatin Ukraine da 'yan bindiga magoya bayan Rasha a birnin Sloviansk.

Karin bayani