Boko Haram ta nuna bidiyon 'yan Chibok

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan matan Chibok da aka sace

Kungiyar Boko Haram ta fitar da sabon bidiyo inda ta nuna 'yan mata dalibai da ta sace, ta kuma ce ba za ta sake su ba har sai an sako mata mayakanta da aka kama.

Shugaban kungiyar, Abubakar Shekau wanda ya yi magana a bidiyon ya nuna 'yan mata kusan 130 sanye da hijabi a wani wuri da ba a sani ba.

Kungiyar ta ce 'yan matan sun karbi shahada watau sun koma bin tafarkin addinnin Musulunci.

A bidiyon da kungiyar ta fitar a ranar Litinin, an nuna 'yan mata uku da aka yi hira da su wadanda suke a firgice, biyu daga cikin 'yan matan sun ce su Kiristoci ne sun koma bin Musulunci.

An nuna 'yan matan a zaune kuma daya daga cikinsu ta ce ba a cutar da su ba.

Bidiyon mai tsawo mintuna 17 ya fito rangadau fiye da sauran bidiyon da 'yan Boko Haram suka saba fitarwa.

A ranar 14 ga watan Afrilu ne 'yan Boko Haram suka sace 'yan mata 276 a Chibok da ke jihar Borno a yayinda kusan 50 suka kubuce.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Karin bayani