Goyon 'Yan hudu a Sansanin gudun hijira

Hakkin mallakar hoto Damien Follet
Image caption Masaya da Taghri da sauran jariransu

Samun 'yan hudu rigis, ba abu ne mai sauki ba. Haka kuma kula da su a sansanin 'yan gudun hijira.

A watan Janairun 2013, wani manomi daga yankin Mole na tsakiyar Mali, Massaya Ag Iliyass, da mai dakinsa, Taghri Walet Tokeye, suka tattara 'ya'yansu shida da 'yan komatsansu suka tsere.

Uku daga cikin yaran sunyi tafiya da kafarsu, sauran kuwa saida suka hau jaki.

Wani abokin Massaya, shi ne ya ba shi aron jaki don daukar kananan yaran, inda sai daya ya hau sannan ya ba dan uwansa.

Ayarin ya shafe tsawon kwana biyar cur yana tafiya ba dare ba rana. Massaya ya ce "tafiya ce mai dan karen nisa da gajiyarwa."

Ya kara da cewar "Dole muka rika tafiya sannu-sannu don kada mu sare, kuma muna zama mu huta sosai-sosai."

Rabin mutanen wannan kauye, su ma duk sun tsere a lokaci guda.

Taghri ta ce "Babu abinci - an washe dukkanin shaguna da kasuwanni."

Ayarin na ficewa ne tare da sojoji da azbinawa 'yan tawaye.

Hakkin mallakar hoto Damien Follet

Ta ce "A cikinsu akwai miyagun mutane da yawa, wadanda ke far wa mutum su yi masa fashi su kwace masa kaya, idan suka bukaci daya daga cikin dabbobinmu muka hana, ba shakka suna iya kashe mu."

Dukkan tawagar na dosar sansanin 'yan gudun hijira na Mbera, da ke yankin kan iyakar Mauritaniya.

Tawagar wani bangare ne na rukunin 'yan gudun hijira dubu 15 da suka isa sansanin a cikin wannan wata kadai.

Lokacin da suka isa, ana cikin yanayi zafi mai tsanani.

Wasu 'yan gudun hijira dubu 60 na kokarin tsira a yanayin zafi na digiri 50 a ma'aunin salsiyus cikin tsakiyar Sahara. Akwai karancin ruwa da abinci.

Cikin dan kankanin lokaci, Taghri ta fuskanci cewa tana dauke da juna biyu, sai dai wannan karo cikin ya banbanta da na baya. Ta ce "Ina iya jin cewa jikina ya kara girma, don haka ga alama akwai wani abu daban."

Hoton cikinta da aka dauka ya bayyana cewa tana dauke da 'yan hudu.

Duk da yanayi zafi mai tsanani da ake ciki, kasancewarta 'yar gudun hijira ya ceci rayuwarta.

Likitoci a sansanin sun cika da doki.

Dr. Kasonga Cheride, wani likita da ke aiki da Kungiyar agaji ta Medecins Sans Frontieres mai kula da ita ya ce "Da ba ma nan, ba shakka tana iya mutuwa, daga ita har jariran da ke cikinta."

Kwanciyar biyu daga cikin jariran ba daidai take ba, don haka sai da aka yi wa mahaifiyar aiki a Bassikounou mai nisan kilomita 17 don a ciro su.

Dr. Kasonga Cheride ya ce "Yanayin wani abin farin ciki ne ga kowa."

Hakkin mallakar hoto Julite Damond
Image caption Sansanin da ake goyon 'yan hudu

Ya ce "Wannan shi ne karon farko da muka taba karbar haihuwar 'yan hudu, don haka muna cike da kwakwar ganinsu… mun cika murna a lokacin da aka haife duka jariran hudu lafiya da cikin aminci."

Mahaifiyar da jariranta uku maza, daya mace sun bar asibiti bayan watanni hudu suna samun kyakkyawar kulawa, inda suka koma sansanin 'yan gudun hijira a yanzu.

Wannan Kalubale ne babba. Ma'auratan da 'ya'yansu 10 suna zaune a daya daga cikin kuntataccen tanti mai zafi.

Massaya ya ce biyu daga cikin 'yan hudu, Fatima da Oumar ba su da fitina, amma Ousmane da Aboubakr, ba sa ji rarrashi - akwai kukan banza, kuma ba sa bari sai an dauke su."

Sauran manyan 'ya'yan shida kuma suna farin ciki da jariran a ko da yaushe suna daukarsu.

Taghri ba ta da tabbas a kan shekarun sauran 'ya'yan nata. Ta ce "Abin da muka sani kawai shi ne shekarar da muka samu danmu na fari."