'Yan ci-rani sun nutse a gabar ruwan Libya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Daruruwan 'yan gudun hijira ne ke jefa rayuwarsu cikin hadari domin ketarawa Turai

Wani jirgin ruwa makare da daruruwan 'yan ci-rani ya nutse a gabar ruwan Libya, a hanyarsa ta zuwa tsibirin Lampedusa na kasar Italiya.

Sojojin ruwan Italiya sun ce sun aika da wani jirgin ruwan yaki da jirgi mai saukar ungulu, domin taimaka wa a kubutar da mutane.

Ma'aikatan wani jirgi da ke aiki a wata rijiyar hakar man fetur a yankin ne suka ba da rahoton kifewar jirgin.

Lamarin ya zo ne bayan jami'an gwamnatin Libya sun bayyana cewa akalla mutane 36 ne suka mutu a ruwa, yayin da wani jirgin ruwan 'yan ci-rani daban ya kife a ranar Talatar da ta gabata.