Nigeria: Shekara guda da dokar ta-baci

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto

Shekara guda ke nan cif-cif tun bayan ayyana dokar ta-baci a yankin arewa maso gabashin Nigeria.

Lokacin da ya ke sanar da ayyana dokar a jihohin Adamawa da Borno da Yobe, Shugaba Goodluck Jonathan ya bayyana cewa sojojin kasar za su yi dukkan mai yiwuwa don kawo karshen cin karen da masu ta da kayar baya ke yi ba babbaka a yankin.

Sai dai kuma ga alama haka ba ta cimma ruwa ba idan aka yi la'akari da karuwar yawan mace-macen da suka biyo baya.

Wadansu alkaluma dai sun yi nuni da cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon rikicin Boko Haram a karkashin dokar ta-bacin ya yi tashin gwauron zabi idan aka kwatanta da wadanda suka rasu kafin nan.

Alkaluman, wadanda wata cibiyar bincike ta Burtaniya ta fitar, sun nuna cewa a shekara guda da aka yi a karkashin dokar ta-bacin, kungiyar Boko Haram ta yi sanadiyyar mutuwar mutane usan dubu biyu da dari biyar--adadin da ya ninka sau biyu idan aka kwatanta da na shekara guda kafin nan.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shekau ya yi barazanar sayar da 'yan matan Chibok sama da 200

Duk da dokar hana fita da katse layukan wayar salula da hukumomi suka yi, mayakan sa-kai dauke da muggan makamai sun yi ta kai hare-hare a yankin na arewa maso gabas.

A baya-bayan nan ma, ta da kayar bayan ya watsu zuwa wadansu sassan kasar, inda musamman a watan jiya wani bam ya tashi a tashar motar Nyanya a wajen babban birnin kasar, Abuja, ya yi sanadiyyar rasuwar mutane fiye da saba'in.

Ita ma hukumar kula da 'yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya, UNHCR, ta ce a daidai wannan lokaci yawan mutanen da ke gujewa rikicin ya karu matuka.

A cewarta, daga watan Mayun bara zuwa yanzu, 'yan gudun hijira dubu shida da dari takwas ne suka tsallaka arewacin Kamaru.

Hukumar ta kuma ce a ko wanne mako, mutane tsakanin dari bakwai da dubu ne ke tsallakwa yankin Diffa a Jamhuriyar Niger.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Alkaluma sun kuma nuna cewa a shekara guda da yankin na arewa maso gabashin Nigeria ke karkashin dokar ta-baci, an lalata makarantu da cibiyoyin ilimi kusan dari.

Karin bayani